Sheikh Na’im Kassim: Idan Duniya Baki Daya Za Ta Taru, Ba Wanda Zai Iya Kwace Makaman Hizbullah

Babban sakataren kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Amurka ta kwana da sanin cewa, za mu kare kanmu, ko da

jagoran Hizbullah

Babban sakataren kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Amurka ta kwana da sanin cewa, za mu kare kanmu, ko da sama da kasa za ta hade.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbulllah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu wanda ya isa ya kwace makaman Hizbullah saboda kare manufofin Isra’ila ko da kuwa duk duniya za ta shelanta yaki akan Lebanon.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma kara da cewa: Ku saurar da kyau ku fahimta! Kasa, da makami da rai, abu ne guda daya, don haka duk wanda yake son kwace abu daya, to dukkanin wadannan guda ukun yake son kwacewa.”

Sheikh Na’im kassim ya kuma ce abinda kwace makamai yake nufi, shi ne shafe samuwarmu, ba kuwa za mu bari hakan ta faru ba.

Babban maatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce: Ba za mu taba yin ko gizau ba akan matsayarmu, domin wannan shi ne matsayi na daukaka, ba kuma da bukatuwa da shaida daga masu aikata laifuka da barna a doron kasa. Ko daga wadanda tarihinsu shi ne haddasa fitina, ko barna.”

Sheikh Na’im Kassim ya ce; Idan kun kashe mu, to jininmu da ya zuba zai tsiro.:

Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Lebanon da ta dakatar da mika kai bori yana hawa a gaban abokan gaba.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Abu daya kawai da abokan gaba suke bukata shi ne Lebanon ta mika wuya, ta zama a karkashin ikon Isra’ila.”

Sheikh Na’im Kassim ya ce; Idan kuwa Lebanon ta mika wuya, to ta gama rushewa, domin ga Syria nan a gabanmu a matsayin misali, duk abinda yake faruwa acan yaudara ce.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted