Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’eem Qaseem ya bayyana matsayin kungiyar a cikin al-amuran siyisa na kasar Lebanon da kuma tattaunawa tsakanin yan kasar Lebanon don fahintar juna tsakaninsu, da kuma zaben shugaban kasa.
A wani jawabin da shugaban kungiyar ta Hizbullah ya yi a yammacin yau Asabar, yace tabo al-amura da dama da suka shafi zamantakewa a kasar Lebanon, da kuma matsayin kungiyarsa.
Yace: Kungiyar zata yi kokarin dabbaka kuduri mai lamna ta 1,701, wanda asalinsa na karshen yakin shekara ta 2006 ne, tsakanin kungiyar da kuma HKI ne.
Daga ciki, kudurin ya bukaci kungiyar ta janye dakarunta zuwa bayan kogin litan na tsakiyar kasar Lebanon, saboda amincin yahudawan HKI a cikin arewacin Falasdinu da aka mamaye.
Dangane da sabuwar gwamnatin kasar Siriya kuma Sheikh Na’eem Kasim ya ce, kungiyar tana fata wa mutanen kasar Siriya alkhairi bayan sauyin gwamnati a kasar, kuma ta san cewa mutanen kasar Siriya ne suke da damar zaben shuwagabaninsu. Amma duk da haka, yana fatan bayan al-amura sun dai-daita a kasar za su sake kulla dangantaka mai kyau da kasar. Sannan ya na fatan sabuwar gwamnatin Siriya, ba za ta amince da samuwar HKI ta kuma samar da huldar jakadanci da ita ba.