Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’eem Qasim ya bayyana cewa kungiyarsa tana sane da taron dangin kasashen yamma da HKI don wargaza kungiyar, amma bata jin tsoron taron nasu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sheikh Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar, wanda kuma aka watsa a tashocin talabijin na masu gwagwarmaya a safiyar yau Talata.
Malamin ya kara da cewa, harshe ba zai iya bayyana irin zafin da suke ji na rashin Sayyid Hassan Nasarallah ba, amma hakan ba zai taba maidasu baya ba.
Yace kungiyar tana kan bakanta na ci gaba da yakin Tufanul Akasa, shekara guda da fara shi. Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ya ce: HKI da kawayenta da yardar All.. ba za su sami nasara a kan kawancen masu gwagwarmaya a yankin ba.
Wannan dai shi ne jawabin sheikh Na’eem Kasim na biyu tun bayan shahadar shugaban kungiyar Sayyeed Hasan Nasarallah yan makonnin da suka gabata.