Sharhin Bayan Labarai: “Karuwar Rikici Tsakanin Island da HKI Dangane Da Yaki A Gaza”

Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu na yau zai yi magana danagne da “karuwai rikici tsakanin kasashen Island da HKI dangane da yaki a

Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu na yau zai yi magana danagne da “karuwai rikici tsakanin kasashen Island da HKI dangane da yaki a Gaza’. Wanda ni tahir amin zan karanta. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Ministan harkokin wajen kasar Iceland Michael Merten ya bayyana cewa bai fahinci abinda HKI take nufi da rufe ofishin jakadancin kasar a birnin Dublin ba, amma abinda ya sani shi ne idan HKI zata bude kofar shiga Gaza, da duniya zata ga abin mamaki sosai saboda girman barna rushe-rushen da HKI a can.

Merten ya kara da cewa, kasar Island sani da cikekken abinda yake faruwa a gaza, sannan a duk matakan da ta dauka zuwa yanzu sun saje da dokokin kasa da kasa, suna kuma kan kuduririn da suka yi magana danagne da kare hakkin bil’adama na kasa da kasa, da dan’adamtaka na kasa da kasa. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu, ba zai iya saurar irin munin abinda yake faruwa a Gaza ba, sannan akwai wasu da dama a kasashen Turai suna kallon irin kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza da idan basirah.

Sannan abinda yake faruwa a yanzu a arewacin Gaza, bai da wani dalili karbebbe wanda ya yi dai-dai da halaye kirki. 

Sannan ya zuwa yanzu dukkan matakan da gwamnatin kasar Island ta dauke dangane da abubuwan da suke faruwa a kasashen gabas ta tsakiya, da kuma gaza, bai fita daga mutunta dokokin kasa da kasa wadanda suka safi kare hakkin bil’adana da kuma mutunta karaman mutum  ba.

Banda haka, a ko yauce mun nanata kuma mun sake nanata cewa muna bukatar tsagaita budewa juna wuta, da kuma musayar mutanen da aka yi garkuwa da su gaba daya, da kuma shigarda kayakin agaji zuwa ga mutanen Gaza.

A ranar lahadin da ta gabata ce, 15 ga watan December, gwamnatin HKI ta rufe ofishin jakadancinta a birnin Dublin, saboda abinda ta kira, siyasar kiyayya ga yahudawa.

Gideon Sa’ar, ministan harkokin wajen HKI, a bayanin da yayi bayan rufe ofishin jakadancin HKI a Dublin, ya tuhumi gwamnatin kasar ta nuna adawa da yahudawa, sannan ya kara da cewa Dublin ta keta dukkan jajayen layin HKI. Sannan sun fahinci cewa, abinda kasar Island take yi, dai-dai yake da kokarin kauda samuwar HKI a doron kasa ne.

HKI dai ta ji zafin matakin da gwamnatin Islanda ta dauka na shiga cikin gungun kasashe wadanda suke goyon bayan kasar Afirka ta Kudu a karar da ta shigar a gaban kotun kasa da kasa ta ICC, wanda ya zama mataki na karshe wanada kasar Island ta dauka, wanda kuma yayi sanadiyyar ketse huldar diblomasiyya tsakanin Dublin da Tel’aviv.

A cikin watan Decemban shekara ta 2023 ne gwamnatin kasar Afirka ta kudu da shigar da kara a gaban kutun hukunta manya-manyan laifuka ta kasa da kasa, inda take tuhumarta da aikata laifukan yaki na kissan kare dangi wa al-ummar Falasdinu a Gaza. Wanda kuma ya sabawa kudurin MDD na shekara ta 1947. Sannan kotun, a ranar 24 ga watan Mayun na wannan shekarar, bayan gudanar da cikekken bincike, ta yanke hukunci, wanda ya bukaci HKI ta dakatar da yaki a garin Rafah na kudancin Gaza. Amma gwamnati HKI ta yi banza da hukuncin kotun wacce take karakshin kula na MDD.

Kasar Island dai tana daga cikin kasashen Turai wadanda suke sukar HKI dangane da kissan kare dangi a Gaza, kuma dauka matakai da dama a kan hakan.

Daga ciki yan majalisar dokokin kasar Islanda a farkon watan Nuwamban shekara ta 2024, ta amince da kuduri wanda ya dauki HKI a matsayin kasa wacce take aikata laifukan yaki wadanda suka hada da kissan kare dangi a Gaza, wannan kuma a gaban kowa a duniya.

Bisa wannan kudurin gwamnatin kasar Isalanda ta sanyawa HKI takunkumai  da dama, wadanda suka hada da dakatar da harkokin kasuwanci da ita, da tafiye-tafiye zuwa kasar da kuma harkokin diblomasiyya.

Banda haka dokar ta bukaci gwamnatin kasar Islanda ta jingine dukkan wata hulda ta sayarwa HKI kayakin aikin soja da kuma makamai ba tare da bata lokaci ba.

Banda haka kasar Island ta haramta sayarwa HKI kayakin da ana iya amfani da su ta bangarori biyu, wato na soja da kuma ta zaman lafiya, haka ma ta haramtawa HKI wucewa da jiragen sama, ko sauka a kan tashoshin jiragen saman na kasar, dauke da makamai.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne Simon Harris firay ministan kasar Islanda ya bada sanarwan cewa, idan fray ministan HKI Benyamin Natanyaho ya kuskura ya taka kasar Iran gwamnatinsa zata kamashi ta mikawa kotun kasa da kasa ta ICC don hukunta shi.

Duk da cewa kasar Islanda tana daga cikin kasashen Turai kuma mamba ne a kungiyar tarayyar Turai, amma dangane da al-amarin falasdinawa, a ko yaushe tana sukar HKI kan irin abinda take aikatawa da falasdinawa, matsayin da babu irinsa a cikin kasashen turai.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments