A wani gagarumin ci gaba, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya ziyarci Tehran domin tattaunawa da mahukuntan kasar.
Wannan ziyara dai ta kasance wani muhimmin ci gimshiki a ci gaba da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, tare da jaddada kudurinsu na tabbatar da gaskiya da ayyukan nukiliya cikin lumana.
Ziyarar dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen turai ke Zarge-zargen Iran da wuce kima a ayyukanta na nukiliya na nukiliya.
Wadannan kasashen sun zargi Iran da kara habaka ayyukanta na nukiliya, suna masu cewa wadataccen sinadarin uranium din kasar ya kai kashi 60 cikin dari.
Iran dai ta yi gaban kanta wajen iyakar tace sinadarin urenum din ta bayan da wasu ɓangarorin suka yi, musamman Amurka, wacce ta janye daga yarjejeniyar nukliliyar da aka cimma da Iran a 2015 bayan zuwan gwmanatin Donald Trump.
Ziyarar Grossi ta ranar 14 ga Nuwamba ta nuna gagarumin sauyi a alakar dake tsakin kungiyar da kuma Iran.
Iran ta kara nuna kyakyawar fatan alheri, ciki har da yarjejeniyoyin da aka kulla da nufin maido da damar jami’an hukumar ta IAEA zuwa muhimman cibiyoyin nukiliya.
Kalaman na ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun jaddada aniyar Tehran na warware takaddama ta hanyar tattaunawa, matukar ba matsin lamba.
Iran ta jaddada kudirinta na ci gaba da yerjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, sannan ta jaddada cewa tana neman hanyoyin samar da makamashin nukiliya cikin lumana, kamar yadda ta dade tana yi.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: A yau duniya ta cimma matsaya kan cewa Iran na son zaman lafiya da tsaro a duniya.
Yana mai cewa, abin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke nema a fannin fasahar nukiliya ya yi daidai da tsare-tsare da lasisin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.
A yayin ganawarsa da Rafael Grossi, shugaba Pezeshkian ya tabo batun ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya da matsayinta na haramcin kera makaman nukiliya.
Ya ce kamar yadda suka sha shelantawa kuma a kan fatawar Jagoran juyin juya halin Musulunci, ba su da niyya kuma ba zasu taba kera makaman kare dangi ba, sannan ba za su taba barin wani ya canza musu wannan manufa ba.
Shugaba na kasar Iran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda suka sha nuna kyakyawar aniyarsu a baya, suna jaddada shirinsu na bada hadin kai da gudanar da hadin gwiwa da kusantar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, domin kawar da shakku da zargin da ake yi kan ayyukan nukiliyar Iran na zaman lafiya da lumana, duk da cewa a yau duniya ta san cewa Jamhuriyar Musulunci tana son wanzuwar zaman lafiya da tsaro.
….
A wani mataki na nuna da gaske take wajen bayyanawa duniya cewa babu wata kumbiya kumbiya game da shirinta na nukiliya Iran, ta baiwa Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliyar Ta Kasa Da Kasa damar Ziyartar wasu Muhimman Cibiyoyinta na nukiliya.
Cibiyoyin da babban daraktan hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA), ya ziyarta sun hada Fordow ( Shahid Ali Muhammad) da Natanz ( Shahid Ahmadi Roshan) a ranar juma’a.
Daga cikin wadanda su ka yi wa Grossi rakiya, da akwai mataimakin shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Behriz Kamalvandi da kuma mataimakin ministan harkokin waje Kazim Gharibabadi.
Rafael Grossi ya ziyarci cibiyoyin ne bayan tattaunawar da ya yi da jami’an gwmanatin Iran da su ka hada da shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan da ministan harkokin waje Abbas Arakci.
Wannan ziyarar ta Grossi ta zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa a tsakanin hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da ta kasa da kasa domin warware rashin fahimtar dake tsakani.
Jami’an gwamnatin Iran sun tabbatar wa da shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran cewa, shirinsu na zaman lafiya ne.
Biga ga abinda wannan ziyarar ta Grossi ke nufi,
Hanyar da ke gaba tana bukatar kwarewa, mutunta juna, da kuma fahimtar hadin kai don hana ci gaba da tabarbarewar dangantaka tsakanin Iran da IAEA
Bayan ziyarar da Darakta Janar Rafael Grossi ya kai Tehran da kuma nuna yadda Iran ta sake bude kofarta ga yin hadin gwiwa, al’ummar duniya sun zura ido su ga yadda hukumar ta IAEA zata yanke hukunci.