Assalamu alikum masu sauraru barkammu da warhaka, barkammu da sake dasuwa a cikin shirimmu na sharhin labarai wanda a yau zai yi magana dangane da ficewar sojojin kasar Iraki kwatakwata daga kasar Iran a karshen watan satumban da ya gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///…A karshen watan satumban shekara ta 2026 da muke ciki ne sojojin Amurka suka fice daga kasar Iraki kwata-kwata bayan mamayar kasar tun shekara 2003. Kuma ficewarsu ya zama wani babban al-amari wanda ya sauya ko kuma zai ci gaba da sauya al-amura a yankin yammacin Asia da kuma duniya gaba daya.
Kimani shekaru 23 da suka gabata, kowa na ganin ba za’a taba samon zaman lafiya a wannan yankin ba, sai tare da kula na Amurka, ammam a halin da kuma ciki wannan al-maran ta zama karya a fili. Ya tabbata ga kowa kan cewa samuwar Amurka a awsu kasashen duniyar sun eke hadda tashe tashen hankula da kuma rashin zaman lafiya.
Banda haka ficewar Amurka a wannan karon bai zo saboda ayyukan diblomasiyya da fahintar juna tsakanin kasar Iran da sauran sojojin da suka mamaye kasar Iraki ba. Sojojin Amurka sun fice daga kasar Iranki ne saboda gwagwarmayar da mutanen kasar Iraki suka yi da su na shekaru masu yawa. Sun fice ne saboda musayar wuta da hare haren da dakarun Hashdushaa bi suka yi ta kai masu a sansanoninsu da ke kasar. Da kuma hakurin mutanen kasar na fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Wani abu mai muhimmanci da ya faru tare da ficewar sojojin Amurka daga kasar Iraki, shi ne wargajewar shirin HKI na Isra’ila babban a yankin. Sojojin Amurka a mamayar kasashe larabawa da ita da kawayenta na kasashen yamma suka yi shi ne don bawa HKI damar fadad HK zuwa mafi yawan kasashen larabawa a yankin Asia ta kudu. Wadanda suka hada da Lebanon Siriya Iraki da saudia. Wanda banda kasashen da wakilansu daga cikin shuwagabannin larabawa suke jagoranta. Irinsu Jordan da saudia da kananan kasashen larabawa na yankin tekun farisa.
HKI ta dogara da Amurka da kuma kawayenta na kasashen yamma don bawa HKI fadada mamayar Falasdinu tare da mamayar wadannan kasashe. A halin yanzu wannan shirin ya fadi ya kuma lalace.
Don haka samuwar sojojin Amurka a kasar Iraki shi ne don gurgunta masu gwagwarmayan ko kawancen Iran a kasar da sauran kasashen larabawa a yankin wadanda suka hada da Hizbullah da Yemen, da kuma bawa HKI mamayar wadannan kasashe. A halin yanzu duk wannan shirin ya rushe.
A cikin shekaru 23 Amurka bata samar da abinda ta yiwa mutanen kasar Iraki na democradiyya da kuma zaman lafiya ba. Sai dai karin rashin zaman lafiya da talauci da kissan kiyashi da ayyukan ta’addanci.
Sannan wani babban al-amari da ya tabba kuma ya bayyana a ficewr sojojin Amurka daga kasar Iraki, su ne amincewan da sauran kasashen larabawa na yankin tekun farisa da kakkafa sansanonin Amurka da kasashen turai a cikin kasashensu saboda neman tsaro kuskure ne babba, wanda suka aikata, kuma a halin yanzu sun rasa wannan amincin. Sun gano cewa tsaro ana samunsa ne , ko ana gina shi ne daga cikin gida kamar yanda JMI tayi.
Iran ta tabbatar wa kasashen Larabawa na yankin suna iya gina tsaronsu daga cikin gida, su kuma magance matsalolin tsaron kasashensu da kansu ko da kuwa kasashe kamar Amurka da HKI ne suke barazana garesu.
Kuma tare da ficewar sojojin Amurka gaba daya daga Iraki wadannan kasashe makobta zasu fahinci cewa ba’a aron zaman lafiya, kuma ba’a sayensa, sai dai ana gina shi ne daga cikin gina, ko kuma tare da hadin kai da kasashen yankin da kuma makobta.
Har’ila yau daga karshe, ficewar sojojinAmurka daga kasar Iraki wata manuniya ce ga wadan nan kasashen larabawa wadanda suke ganin samar da hulda da HKI ko kuma amincewa da shirin ‘Sulhun Abraham’ ba zai taba samar da zaman lafiya mai dorewa a wa kasashensu ga kuma yankin ba. Wannan ba karamin kuskure ne da suka aikata kuma a halin yanzu suna dandana zafin hakan.
A wani bangare kuma rundunar Quds na IRGC ta JMI ta bada sanarwan cewa ficewar sojojin Amurka daga kasar Iraki, darasi ni babban ga shiekhunan kasashen larabawa kan cewa sojojin kasashen waje a cikin kasashensu ba abar amincewa bane.
Don ba abinda suke yi inbanda harkokinsu na dada saku dogara da su da kuma samar da karin tashe tashen hankula a cikin kasashenku.
Har’ila yau wannan babban darasine ga Falasdinawa, saboda su san cewa, ko menene dadewar mamayar, kuma ko menene karfin masu mamaya ba zasu dawwama ba, dole ne wata rana, tare da gwagwarmaya zasu fice daga kasarku.