A wannan Lahadin ce bababn hafsan hafoshin sojin kasar Saudiyya tare da wata bababr tawaga ta jami’ai daga ma’iaktar tsaron kasar ta Saudiyya suka kai ziyarar aiki a kasar Iran.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri, ya tattauna da takwaransa na Saudiyya, Laftanar Janar Fayyad bin Hamed al-Ruwaili, kan hanyoyin inganta diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya.
Tun da farko kanfanin dillancin labaran Iran Tasnim ya bayyana cewa al-Ruwaili tare da wata babbar tawagar sojojin Saudiyya sun isa birnin Tehran a safiyar Lahadi a wata ziyarar aiki ta musamman da suka kai kasar Iran.
A cikin shekarar da ta gabata, Bagheri ya tattauna ta wayar tarho da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman, inda suka mai da hankali kan halin da ake ciki a yankin, da inganta hadin gwiwar tsaro tsakanin sojojin kasashen Saudiyya da Iran, da kuma tinkarar muhimman batutuwan da suka shafi kasashen musulmi.
Hakan ya biyo bayan dawo da huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu ne a watan Maris din shekarar 2023.
A yayin ziyarar ta bababn hafsan hafsoshin sojin kasar Saudiyya a birnin Tehran, manyan jami’an sojin kasashen biyu sun yi doguwar tatatunawa a kebe, duk kuwa da cewa babu wani Karin bayani kan abubuwan da aka tattaunawa a kebe tsakanin manyan jami’an sojin kasashen biyu, amma dai da dama daga cikin masana a kasashen biyu sun yi imanin cewa, lamarin baya rasa nasaba da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da wajabcin hada karfi da karfe tsakanin manyan kasashen biyu na musulmi, domin tunkarar manyan kalubale da ke a agaban al’ummomin yankin gabas ta tsakiya ta fuskacin tsaro da kuma batutuwa na ayyukan hadin gwiwa a tsakaninsu.
A watan Oktoba ne Saudiyya ta sanar da cewa za a gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa tsakaninta da Iran da sauran kasashe a tekun Oman.
Baya ga haka kuma, gwamnatocin kasashen biyu na Iran da Saudiyya, sun tabbatar da cewa ana samun ci gaba cikin sauri dangane da yadda alaka a tsakaninsu take ci gaba da kara habaka a dukkanin bangarori.
Tun bayan dawo da huldar diflomasiyya a tsakaninsu, Saudiyya da Iran sun cimma yarjeniyoyi daban-daban, da hakan ya hada da bangarorin kasuwanci, da ziyara, da kuma gudanar da ayyuka na hadin gwaiwa a bangarori na ilimin kimiyya da fasaha, wanda kasashen biyu za su iya cin moriyar juna kan hakan.
Baya ga haka kuma, akwai babtutuwa da suka shafi batun halin rashin tabbas a yankin gabas ta tsakiya, wanda a matsayinsu na manyan kasashen yankin mafi tasiri, za su iya taka gagarumar rawa wajen samar da mafita, da kuma yin abin da zai taimaka wajen samun damar magance matsaloli da dama da yankin ke fama da su.
Saudiyya da Iran sun gudanar da tattaunawa domin daukar matakai na hadin gwiwa domin ganin an dakile ruruwar wutar yaki a yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma har a fara ganin sakamakon hakan, inda a baya-bayan nan a lokacin da Haramtacciyar kasar Isra’ila ke hankoron kaiwa Iran harin, Saudiyya ta sheda wa Amurka da Isra’ila cewa ba za ta taba bari a yi amfani da sararin samaniyarta ko wani bangare na kasarta domin kaiwa kasar Iran hari ba.
Wanda hakan tabbas yana nuni da wani babban sauyi da aka samu a cikin salon siyasar gwamnatin Saudiyya game da kasar Iran. Baya ga Saudiyya ma, hatta sauran kasashe masu yin biyayya ga Saudiyya sau da kafa, kamar su UAE, da Bahrain, duk sun bayyana irin wannan matsaya, wanda kuma tabbas hakan yana da alaka ne da sauyin da aka samu daga ita kanta Saudiyya din dangane da siyasarta a kan kasar Iran.
Daga cikin dalilai da ake ganin cewa sun tasiri wajen sanya Saudiyya ta canja matsayarta dangane da Iran, har da muhimmiyar rawa da taka ne wajen shiga tsakani da kuma sasanta Yemen da Saudiyya, wanda hakan shi ne ya kawo karshen yakin da aka kwashe tsawon shekaru ana gwabzawa tsakanin Saudiyya da Yemen.
Kasashen Iran da Saudiyya suna da matukar muhimmanci da bababn tasiri a yankin gabas ta tsakiya, ta yadda hadin kai da hadin gwiwa a tsakaninsu zai iya zama babban karfe kafa da zai hana kasashe masu girman kai cimma manufofinsu a gabas ta tsakiya da kuma kasashen larabawa da na musulmi, musamman ma ganin cewa dukkanin matsaloli da ake ahifarwa kasashen musulmi suna da nasaba ne da baraka da ake samu da kuma rashin haduwar baki a kan batutuwa da dama a tsakanin kasashen musulmi, kamar yadda masu iya Magana ke cewa, sai bango ya tsage ne kadangare kan iya samu wurin da zai shiga.
Baya ga haka kuma irin wannan hadin gwiwa tsakanin Iran da Saudiyya zai taimaka matuka wajen kara kusanto da musulmi da hada kansu wuri guda, tare da yin abin da ya rataya a kansu a matsayinsu na al’umma guda daya wadda take da babban tasiri a duniya, wanda kuma tasirin musulmi ya dusashe ne e a duniya sakamakon rarrabuwar kawuna da kuma yadda makiya musulunci suka kutsa a tsakaninsu suka raba kansu kuma suka tarwatsa su.
A halin yanzu dai wannan sabon yunkuri tsakanin Saudiyya da Iran yana a matsayin wata bababr fata ta haduwar kawuna tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma na musulmi, wanda kuma tabbas zai tasiri wajen magance da dama daga cikin manyan matsaloli da kalulbale da ke a gaban duniayr musulmi, musamman batutuwan da suka fi ci musu tuwo a kwarya, daga cikinsu batun Falastinu da sauran batutuwa na yankin gabas tasakiya.