Falasdinawa biyar ne suka yi shahada a wani harin bam da sojojin Isra’ila suka kai kan wani gida a yammacin birnin Gaza
Majiyoyin lafiya sun shaida wa manema labarai cewa: Falasdinawa biyar ne suka yi shahada wasu kuma sunka jikkata a wani harin jirgin sama da sojojin mamayar Isra’ila ya kai kan wani ginin gidaje a yammacin birnin Gaza da safiyar Asabar.
Kafafen yada labaran Falasdinawa sun ruwaito cewa: Jiragen yakin sojin Isra’ila sun kai hare-hare kan wasu wurare a yammacin birnin Gaza, yayin da sojojin mamayar na Isra’ila suka kai hare-haren rushe-rushen a unguwar Tuffah da ke gabashin birnin.
Wata majiyar lafiya ta bayyana cewa: Shahidai sune Maysaa Abu Daoud (mai shekaru 55) da ‘yarta Mariya Abu Daoud (mai shekaru 36), ban da Yasmin Al-Boubou (mai shekaru 48), Haloum Al-Boubou (mai shekaru 23), da kuma matashin Bilal Ali Awda (mai shekaru 20).