Tun a cikin watan Disambada ya wuce ne daliban jami’an Shekin Anta-Diop na kasar Senegal suke Zanga-zanga akan neman gwmnatin kasar ta ci gba da daukar nauyin yin karatunsu, wanda ya kai su ga yin taho mu gama da jami’an tsaro.
A jiya juma’an an sake samun wani hargitsin a cikin jami’ar, kuma wasu Karin jami’o’in kasar sun bi sahun yin Zanga-zanga.
Wani dalibi na jami’ar Sheikh Anta-Diop ya fada wa manema labaru cewa, rabon da a biya su kudin taimakon da gwamnati take ba su, an dauki watanni 13, don haka ba za su iya ci gaba da jurewa halin da ake ciki ba.
A farkon watan Disamba na 2025 ne dai daliban jami’a su ka hau kan titunan suna yin Zanga-zanga saboda jinkirin biyansu hakkokinsu na lokaci mai tsawo.
Daliban sun rika jefawa ‘yan sanda duwatsu, yayin da su kuma su ka rika watsa musu hayaki ma isa hawaye.
A jiya Juma’a yanayin ya kara tsanani bayan da hukumar da yake kula da jami’o’in su ka sanar da rufe dakunan cin abinci da suke a cikin harabobin jami’o’in. Daliban sun bayyana wannan matakin da cewa wata makarkashiya ce da aka kitsawa daliban.
Wannan matakin ya ingiza daliban sauran jami’oi su ka fito kan tituna domin yin Zanga-zanga da hakan ya haifar da taho mu gama da ‘yan sandan.