Jagoran Ansarullah na kasar Yemen ya bayyana cewa batun kasar Yemen ba na ‘yan Husy ba ne, batu da ya shafi al’ummar kasar baki daya,tare da yin kira ga duniya da ta fahimci hakan.
Sayyid Abdulmalik al-Husy ya kuma jaddada cewa al’ummar Yemen za su ci gaba da riko ba da kare hakkokinsu da su ka hada kare hakkokin al’ummar Falasdinu, tare da jan kunnen kasashen Turkiya da Pakistan da wasu kasashe akan kar su goyi bayan Saudiyya akan Yemen.
Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya kuma yi Ishara da yadda yanayin rayuwa a kasar ta Yemen ya tabarbare saboda killace kasar da Saudiyya ta yi. Haka nan kuma ya bayyana yadda Yemen ta fuskanci wani budadden makirci na Saudiyya wanda ya kunshi aikewa makamai masu yawa a karkashin jagorancin kwanadojin sojan Saudiyya.
Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kara da cewa;kwamandojin sojan Saudiyya ne suke jagorantar yaki a cikin gundumomin Yemen da zummar mamaye ta.
Sayyid Abdulmalik Husi ya kuma ce; Abinda Saudiyya take so shi ne dukkanin duniya ta taya ta yaki akan Yemen. Sai dai kuma ya ce; duk kasar da ta taya Saudiyya yaki to za ta ci kasa, kuma zai dauki alhakin duk wani laifi da za a tafaka akan al’ummar Yemen.
Sayyid Abdulmalik Husi ya kuma ce; Al’ummar Yemen suna yaki ne akan batu na adalci,kuma abinda suke nema shi ne a yi musu adalci,don haka kamata ya yi ace duk wanda zai tsoma baki, to ya yi hakan domin tabbatar da gaskiya.