Sayyed Fadlullahi ya taya al’ummar Falastinu murnar tsayin dakansu da gwagwarmayarsu a fagen kare kai
Sayyed Ali Fadlullahi ya taya al’ummar Falastinu murnar nasarar da suka samu ta hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunonin tsakaninsu da gwamnatin mamayar Isra’ila, lamarin da ya ba da damar dakatar da zubar da jini da rusa Gaza, duk da cewa har yanzu gwamnatin makiya ‘yan sahayoniyya tana karya yarjejeniyar da aka cimma da ita, domin tana son samun ƙarin riba da kuma nuna kanta a matsayin wanda ta mallaki hukuncin ƙarshe kan batun yakin.
Shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-Manar ya ruwaito cewa: Sayyed Ali Fadlullahi ya bayyana hakan ne a cikin hudubar sallar Juma’a daga kan mumbarin Masallacin Imamaini Al-Hassanaini (a.s) da ke yankin kudancin birnin Beirut, inda ya jaddada cewa: “Sun yi imanin cewa wannan nasara ba za ta kasance ba, ba don tsayin dakan ‘yan gwagwarmaya da goyon bayan sojoji da ‘yan siyasa da kuma al’umma da ta sadaukar da mafi kimar abin da ta mallaka ba daga gagarumin goyon bayan Falasdinawa da sadaukarwarsu mai girma ba.”