Sarkin kasar Saudiya Salman bin Abdulaziz da kuma yerima mai jarin gadon sarauta kuma Firaiministan kasar Muhammad bin Salman duk sun aike da sakon taya murna ga zabebben shugaban kasar Iran Masa’ud Pezeskiyan saboda zabensa a matsayin shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto sakon da shugabannin biyu suka aikawa Pezeskiya a jiya Asabar jim kadan bayan an bada sanarwan nasararsa a matsayin zabebben shugaban kasar Iran a nan Tehran.
Saudiya ta yi fatan alkhairi da lafiyan jiki ga zabbben shugaban kasar, sannan ta kara da cewa a shirye suke ta ga kasashen biyu, yan’uwa sun ci gaba da kyautata dangantaka a tsakaninsu, musamman a bangarorin tsaron a yankin Asaiya ta kudu da kuma duniya gaba daya.