Sanatan Amurka Mai Ruruta Yaki Ya Bukaci Trump Ya Daina Sauraron Kowa Ya Farwa Iran Da Yaki

Sanata Lindsey Graham mai ruruta a yaki dan Jam’iyyar Republican ya bukaci shugaban kasar Amurka Donal Trump ya daina sauraron masu tsoratar da shi kan

Sanata Lindsey Graham mai ruruta a yaki dan Jam’iyyar Republican ya bukaci shugaban kasar Amurka Donal Trump ya daina sauraron masu tsoratar da shi kan yaki da Iran, ya kuma yi sauri y agama da ita.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shafin labarai na Axios na Amurka ya nakalto Graham yana fadar haka. Graham ya bayyana cewa ya fahinci cewa, yaki a yanking abas ta tsakiya a halin yanzu yana da matukar hatsari, amma kuma ba za’a bar sharri ya ci ga ba ba.

Sanatan  ya kara da cewa yana fadar akwai damar Amurka ta kafa tarihi da kauda JMI daga doron kasa, da kuma babban sauyi a duniya. Ya ce ya fahinci cewa, muryoyi da suke tasowa don hana yaki aukuwa suna kara yawa, amma kuma muna jira mu ga yadda al-amarin zai yi aiki.

Gwamnatin Trump ta sha alwashin sauya gwamnatin kasar Iran, bayan da mayakan Daesh da suka aika cikin kasar sun kasa kifar da gwamnatin kasar a farkon wannan shekarar.

A halin yanzu dai akwai jairagen ruwan yakin Amurka wadanda ake kira Carries a yankin don shirin farwa kasar da yaki a ko wani lokaci nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted