Sabon Rahoton Amurka: Iran Ta Rusa Da Lalalta Jiragen Yakin Amurka 81

A wani sabon rahoto da cibiyar bincike ta majalisar Amurka ( congress) ta fitar, ya tabbatar da cewa a yaki da Iran Amurka ta yi
jirgin saman amurka na yaki

A wani sabon rahoto da cibiyar bincike ta majalisar Amurka ( congress) ta fitar, ya tabbatar da cewa a yaki da Iran Amurka ta yi asarar jiragen sama mabanbanta da sun kai 81 da kudinsu ya kai dala biliyan 3.3.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Adadin jiragen yakin da masu saukar angulu da kuma marasa matuki da Iran ta rusa da kuma lalatawa a tsawon watannin yaki, sun kai 81.

Haka nan kuma rahoton ya ce Daga cikin jiragen da yaki da Iran din ya lalata da akwai jirage samfurin  F-15 guda 12 da ake kira “Strike Eagle” daga cikinsu da kawai guda 3 da aka harbo a kasar Kuwaiti.

Haka nan kuma jirgin F-35 guda daya, da kuma jirage biyu samfurin “Thunder-Bolt” da kuma jiragen K-C 135 guda 7 da ake amfani da su wajen zubawa jiragen sama man fetur.

Haka nan kuma yaki da Iran ya rusa jirgin Amurka samfufin “I-3 center” wanda aikinsa shi ne yin gargadi idan wani hatsari ya tunkaro, sai dai bai iya kare kansa ba.

Wani sashe na wannan rahoton ya kuma ce, wannan rahoton na bayan nan baya nufin cewa  iyakar asarar da Amurkan ta yi kenan a fagen jiragen sama na yaki, bincike zai iya fita da kari.

A tsakiyar yakin dai Amurka ta yi ta kokarin boye yawan asarar da ta fuskanta, musamman ma dai jiragen yakin da take ji da su, da su ka hada F-16- da F-35.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted