Rahotanni sun ce wani sabon fada ya barke tsakanin Sojojin Habasha da Yan tawayen Tigray na TPLF wadanda ke iko da yankin na arewacin kasar, lamarin da ya jefa fargabar yiwuwar dawowar yakin kusan shekaru 4 bayan cin nasarar kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.
Da asubahin jiya Asabar ne aka fara sabon fadan bayan da sojoji suka kaddamar da hare-hare kan mayakan ƴan tawayen da ke Shererina a yammacin yankin na Tigray mai iyaka da Sudan, inda aka rika jiyo karar harbe-harbe da fashe-fashe kodayake ya zuwa yanzu gwamnatin Addis Ababa bata ce komai akan sumamen dakarun nata ba.
Tsawon watanni aka shafe bangaren ƴan tawayen na Tigray da kuma gwamnatin kasar ta Habasha na girke mayaka a kan iyakar yankin na Tigray lamarin da ya sanya kowanne bangare zargin dan uwansa da kokarin tayar da rikici.
Wasu mutane sun shaidawa AFP cewa har zuwa safiyar yau Lahadi ana ci gaba da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu kuma dukkaninsu na amfani da manyan makamai a yammacin na Tigray yankin da ake takaddama akan shi tsakanin mahukuntan Habasha da ƴan gwagwarmaya masu ikirarin kishin yankin Amhara.