Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci {IRGC} Ta Sanar Da Kakkabo Jirgin Saman Amurka

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da harbo wani jirgin saman Amurka mara matuki kirar MQ-9 Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da harbo wani jirgin saman Amurka mara matuki kirar MQ-9

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da safiyar yau Laraba cewa ta harbo wani jirgin saman Amurka kirar MQ-9 Reaper a sararin samaniyyar lardin Bushehr da ke kudancin Iran.

A cikin wata sanarwa a hukumance, ofishin hulda da jama’a na IRGC ya tabbatar da cewa: Rundunar tsaron sama sun gano kuma sun kakkabo jirgin Amurka mara matuki ciki yayin da yake kokarin kusantar yankin da kuma tsoma baki a cikin rikicin da ke ci gaba da faruwa a arewacin Tekun Farisa.

Sanarwar ta bayyana cewa: Tsarin tsaron sararin samaniya na IRGC ya kai hari kan jirgin saman mara matuki ciki a birnin Jam da ke lardin Bushehr, wanda ya haifar da faduwarsa da kuma lalata shi gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted