Rundunar sojin Yemen ta sanar da cewa: A karo na goma ta samu nasarar harbo wani jirgin Amurka MQ-9
Rundunar sojin Yemen ta bayyana cewa: Dakarun tsaron saman Yemen sun harbo wani jirgin saman Amurka “MQ_9” ta hanyar makami mai linzami kirar kasa zuwa sama a lokacin da jirgin saman na Amurka yake gudanar da ayyukan wuce gona da iri a sararin samaniyar lardin Dhamar da ke nisan kilomita 100 da kudancin birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen.
Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya bayyana a yau Litinin ta hanyar gidan talabijin din kasar cewa: Da taimakon Allah, sojojin tsaron saman kasar sun samu nasarar harbo wani jirgin Amurka “MQ_9” da wani makami mai linzami a cikin gidan Yemen a lokacin da jirgin yake shawagi a sararin samaniyar kasar ta Yemen musamman a sararin samaniyar lardin Dhamar da ke tsakiyar kasar.
Birgediya Janar Sari’e ya yi nuni da cewa: Jirgin da aka harbo a sararin samaniyar lardin na Dhamar shi ne na uku a cikin mako guda kuma irin wannan nau’in jirgin na goma tun bayan fara ayyukan tallafawa Gaza.