Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran ya jaddada cewa: ramuwar gayya a kan haramtacciyar kasar Isra’ila aba ce da ba makawa kan ta
Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa daukar fansa kan jinin shahidi Isma’il Haniyyah ta hanyar mayar da martani kan yahudawan sahayoniyya abu ne da babu makawa kansa kuma tabbas.
A jawabinsa a yayin bikin karrama da kumakaddamar da sabon ministan tsaron kasar, Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta fada tarkon yaudara da tsokanar makiya ba.
Kamar yadda Manjo Janar Baqiri ya yi nuni kan irin halin da yankin ke ciki bayan harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsa, yana mai cewa: A cikin watanni 11 da suka gabata, al’amura da dama sun faru a yankin yammacin Asiya, ciki har da harin Ambaliyar Al-Aqsa da harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Damascus, da kuma harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na Alkawarin Gaskiya, kisan gillar da aka yi wa shahidi Isma’il Haniyyah, da kuma matakin ramuwar gayya na Hizbullah a martanin farko na kisan gillar da aka yi wa Fouad Shukr.