Rundunar Kassam ta kungiyar Hamas, ta sanar da kai wa dandazon sojojin HKI sabbin hare-hare guda biyu; Daya a yakin Tal-Sultan, sai kuma wani a “Shuja’iyyah” inda ta kashe tare da jikkata sojoji 10.
Sanarwar kungiyar ta Hamas ta kuma ce; sun yi amfani ne da makamai mabanbanta akan sojojin HKI da su ka hada manyan bindigogi, da kuma rokoki.
Har ila yau, sanarwar ta Hamas ta ce; A sanadiyyar harin da su ka kai, sun yi nasarar kashe da jikkata sojojin abokan gaba masu yawa.