Kamfanin dallancin labarun “Reuters” ya nakalto cewa; mahukuntan Saudiyya sun ki amincewa da su bai wa Isra’ila damar aikewa da jirgin yaki zuwa filin saukar jiragen sama na Tabuka domin daukar matafiya yahudawa fiye da 100 da suke cikin jirgin “Fly-Dubai” da ya yi saukar gaggawa.
Wata majiyar ta fada wa kamfanin dillancin labarun “Reuters” cewa; Jirgin sama na yaki na HKI yana Shirin tashi daga Tel Aviv domin ya nufi Saudiyya ya dauko matafiya yahudawa 150 da suke cikin jirgin da ya yi saukar gaggawa.
Wata majiyar ta ce; An yi fada ne a cikin dakin tukin jirgin a tsakanin matukin jirgin da mataimakinsa, wanda ya yi kokarin caka masa wuka, domin kwance sarrafa jirgin saboda ya kai hari a wani wuri.
Ya zuwa yanzu dai masu bin diddigin abinda ya faru sun shakku akan riwayar da ta fito daga HKI akan gaskiyar lamarin.
A kowace rana kamfanin jirgin “Fly-Dubai” yana zirga-zirga tsakanin Dubai da Tel Aviv yana kuma wucewa ne ta samaniyar kasashen Saudiyya da Jordan.