Red Cross: Asibitocin Kasar Yemen Suna Fuskantar Rashin Kayan Aiki

Kungiyar Agaji ta “Red Cross” ta sanar da cewa da akwai nakasu na kayan aiki a cikin asibitocin kasar Yemen wacce a halin yanzu take

lambar kungiyar agaji

Kungiyar Agaji ta “Red Cross” ta sanar da cewa da akwai nakasu na kayan aiki a cikin asibitocin kasar Yemen wacce a halin yanzu take fama da yaki, haka nan kuma da akwai cunkuson marasa lafiya a cikinsa.

Kungiyar ta kuma ambaci yadda ake yawan samun wadanda suke jikkata a filin daga da suke zuwa asibitocin da su ka fi kusa da wurin yaki wanda yana kaiwa sau 700 a cikin mako daya.

A gefe daya kamfanin dillancin labarun “Sabaa’ na kasar Yemen ya bayana cewa, a tsawon lokacin da Saudiyya ta rika kai wa kasar Yemen hare-haren ta lalata gidajen mai 571 a fadin gundumomin kasar, da kuma motocin jigilar mai guda 644.

Haka nan kuma ta ce; hare-haren na Saudiyya sun nufi unguwannin farafen hula da kasuwanni da asibitoci  da makarantu har sau 3000.

Haka nan kuma ta yi Ishara da wasu hare-haren na Saudiyya da su ka shafi wuraren aure da inda ake yin zaman makoki da hanyoyi da gadoji. Bugu da kari hare-haren na Saudiyya sun hada sansanonin ‘yan hijira da filayen jiragen sama da na tasoshin ruwa da kuma masana’antu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted