Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta kira yi kasar jamus da ta yarda cewa, laifukan da ‘yan Nazi su ka yi a Leningrad kisan kiyashi ne,domin sun kashe mutane ta hanyoyin yaki da yunwa da sun kai 800,000.
Kamfanin dillancin labarun “Sputnik’ na kasar Rasha ya sami kwafin takardar da ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta aike wa ofishin jakadancinta dake Jamus, da aka bayyana cewa; Rasha tana daukar killace Leningrad da laifukan da jamus ta tafka a cikin tarayyar Soviet a yayin yakin duniya na biyu, da cewa ayyuka ne na kisan kiyashi akan al’ummun tarayyar.”
Har ila yau, takardar ta ce kotun birnin Saint Petersburg ta yi hukunci a ranar 20 ga watan Oktoba 2022 dake cewa abinda ya faru din kisan kiyashi ne.
Kasar Rasha dai tana son ganin Jamus ya yarda da cewa lallai ta tafka laifukan yaki da kisan kiyashi a wancan lokacin.
A yayin yakin duniya na biyu ne dai jamus ta kai wa Soviet harin da ta bai wa sunan: Barbarosa’ wanda ya fara daga ranar 22 ga watan Yuni 1941. Harin dai ya kare da killace yankin Leningrda-wato garin Petersburg a yanzu.
Bayan da Jamusawa su ka kasa kutsawa cikin garin, sun killace shi da hana shigar da duk wani abu mai amfani a cikinsa, da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 800,000.