Rasha ta jaddada goyon bayanta ga halaltattun haƙƙoƙin Iran a tattaunawar makamashin nukiliya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta sanar da cewa: Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi magana ta wayar tarho da Ministan Harkokin Wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi a ranar Juma’a.
Ma’aikatar ta bayyana cewa: Lavrov da Araqchi sun yi musayar ra’ayoyi kan batun makamashin nukiliya a yayin tattaunawan.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kuma sanar da cewa: Lavrov, a lokacin kiran da ya yi da Araqchi, ya jaddada goyon bayan Rasha ga tsarin tattaunawar da nufin neman mafita mai adalci da kuma girmama haƙƙoƙin Iran.
Abin lura a nan shi ne cewa: Sergey Lavrov, Ministan Harkokin Wajen Rasha, ya bayyana a ranar Laraba a wata hira da wata tashar Saudiyya cewa: Amurka da Isra’ila sun aikata wani mummunan aiki ta hanyar kai hari kan wuraren makamashin nukiliyar Iran, yana mai nuni da cewa: Iran ta daɗe tana bayyana alƙawarinta na amincewa da Yarjejeniyar hana yaɗuwar Makaman nukiliya.