Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana shirinta na taimakawa wajen nemo jirgin shugaban kasar Iran mai saukar ungulu
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta sanar da cewa: Rasha a shirye take ta ba da taimakon da ya dace wajen neman jirgin shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da kuma binciken musabbabin hatsarin jirgin da ke dauke da shi da kuma tawagarsa.
A cikin wata sanarwa da Zakharova ta fitar ta bayyana cewa: Suna bin bayanan da ke fitowa a hankali game da makomar fasinjojin jirgin mai saukar ungulu mai dauke da manyan jami’an Iran ciki har da shugaba Ra’isi. Tana mai jaddada cewa: Rasha a shirye take ta ba da dukkan taimakon da ya dace wajen neman jirgin da ya bace da kuma binciken musabbabin faruwar hatsarin. Ta kara da cewa: Suna fatan jami’an suna raye kuma lafiyarsu ba ta cikin hadari.