Search
Close this search box.

Rasha: Putin Yace ‘Mosco’ Zata Dauki Mataki Irin Wanda Kasashen Yamma Suka Dauka’ Idan Ukraine Ta Kai Hare Hare Da Makamansu Kan Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gargadi kasashen yamma kan cewa idan sun bawa kasar Ukraine damar kai hare hare cikin kasar Rasha da makamansu,

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gargadi kasashen yamma kan cewa idan sun bawa kasar Ukraine damar kai hare hare cikin kasar Rasha da makamansu, Mosco zata maida martani da irinsa, wato zata bawa makiyan wadannan kasashe a inda ake yaki das u don amfani da makaman Rasha kansu a ko ina a duniya.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Laraba a taron kafafen yada labaran da ya halarta a birnin St. Petersburg inda ake taron tattalin arziki na shekara-shekara da aka saba gudanarwa a kasar.

Shugaban ya kara da cewa hakkin Mosco ne ta bawa wasu kasashe makamai irinsu, don su yi amfani da su ko su kai hare hare kan bukatun kasashen yamma, kamar yadda kasashen suke yi a Ukraine.

Yace: Idan wasu suna ganin zasu yi wani abu don rikata  al’amurammu, me yasa mu ba zamu yi haka ba?’

Daga karshe shugaban yayi tir da izinin da wasu kasashen yamma suka bawa kasar Ukraine na ta yi amfani da makamansu don kai hare hare cikin kasar Rasha.

Kafin haka dai, a karshen watan mayun da ya gabata ne, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bawa kasar Ukraine izinin  amfani da makamai masu linzami wadanda kuma suke cikin dogon zango wadanda ta bawa kasar don cillasu cikin kasar Rasha.

Ba’a dade da sai gwamnatin kasar Jamus ta ce itama ta bawa kasar Ukraine damar amfani da makamai masu linzami na kasar Jamus don amfani da su kan kasar Rasha. Sai kuma kasashen Faransa da Burtaniya wadanda tuni sun rika sun bawa Ukraine wannan damar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments