Kasar Rasha ta fara tsare-tsaren yadda zata ginawa kasar Mali hukumar kula da sararin samaniya da kuma tashar sararin samaniya.
Kamfanin Roscosmos,mallakar gwamnatin Rasha, zai ba da gudummawarsa ga samar da wannan hukumar, yayin da za a horar da kwararrun ‘yan Mali a Moscow a karkashin wata yarjejeniya daban.
Tawagar Rasha ta duba wurare da dama da suka dace da gine-ginen hukumar sararin samaniya ta Mali, da kuma tashoshin sadarwa ta tauraron dan adam.
Manufar ta samo asali ne daga kwangilar da aka sanya hannu a ranar 23 ga watan Oktoba tare da Kamfanin Mali mai kula da tafiyar da irin wadanan ayyukan na(SMTD-SA).
Wannan yarjejeniya ta kunshi ayyukan bincike da ba da shawara don kirkirar hukumar.
An cimma Yarjejeniyar Babban Daraktan Ilimi da Binciken Kimiyya na Mali a Cibiyar Jiragen Sama ta Moscow (MAI), Kafin daga bisani Ƙwararrun Glavkosmos sun tattauna wannan a Bamako tare da masana da masu bincike na Mali.
Wannan dai na daga cikin burin kasar Rasha na fadada hadin gwiwarta da Afirka.
A gefen taronsu karo na uku a Moscow ranakun 28 da 29 ga Oktoba Mali ta sanya hannu kan kwangiloli biyu da Rosgeo, wani kamfani mallakar gwamnatin Rasha wanda ya kware a fannin ilimin kasa.
Na biyu zai ba da damar hada bayanai kan albarkatun kasa, a cewar Ma’aikatar Ma’adinai ta Mali.