Kakakin Fadar Kremlin na kasar Rasha Dmitry Pescov ya yi karin bayani kan yarjeniya mai muhimmanci tsakanin kasarsa da kuma JMI.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa wannan yarjeniya mai muhimmanci don biyan bukatun kasashen biyu ne, kuma bai da dangantaka da hada kai don yakar wata kasa ko cutar da wata kasa.
Kamfanin dillancin laraban IP na kasar Iran ya ce shugaban kasar Rasha Vlamir Putin ya ce manufar wannan yarjeniyar don amfanin kasashen biyu ne kawai kuma baida dangantaka da wata kasu ko kasashe. Y ace yarjeniya ce ta aiki tare don amfanin kasashen biyu a bangarori da dama wadanda suka hada da tsaro, siyasa, kasuwanci, tattalin arziki, fasahan zamani, ilmi, al-adu da kuma ayyukan jinkai da sauransu.
Peskov ya ce dangane da lokacin sanya hannu a yarjeniyar, shi ma bai da dangantaka da shigowar sabuwar gwamnati a kasar Amurka. Gamu da katar ne hakan ya kasance. Yace yarjeniyar da za’a sanyawa hannu a gobe Alhamis kokari ne na fahintar juna a tsakanin kasar biyu, kuma a yanzun ne suka kai marhalar sanya hannu a knasu.
Kakakin fadar Kremlin y ace hatta bayan sanya hannu a kan wannan yarjeniyar kasashen biyu zasu ci gaba da tattaunawa a kan wasu al-amura cikin wannan yarjeniyar da kuma wasu daga wajenta.
Jakadan kasar Iran a Rasha Kazzem Jalali, ya kara da cewa yanjeniyar ta kunshi al-amura guda 47 wandanda kasashen biyu zasu yi aiki tare a tsakaninsu don amfanar juna. A yau Laraba ce aka saran shugaba Masoud Pezeshkiyan zai isa birnin Mosco don sanya hannu a kan wannan yarjeniyar.