Rasha Da China, Sun Karfafa Dangantakar Dake A Tsakaninsu

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping sun amince su kara zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, tare da tsawatar

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping sun amince su kara zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, tare da tsawatar wa Amurka kan yin barazana ga kasashensu.

Putin wanda ya isa kasar Sin a ziyararsa ta farko bayan da aka rantsar da shi a karo na biyar a matsayin shugaban kasar Rasha a farkon wannan wata, ya gana da takwaransa Xi, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da tattalin arziki, tsaro, Ukraine.

Shugabannin sun nanata tsananin damuwarsu kan yunkurin Amurka na kawo cikas ga daidaiton tsaro a yankin,” in ji sanarwar hadin gwiwa da aka fitar.

Kasar Sin, da Rasha sun karfafa hadin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki da huldar diflomasiyya sosai a cikin ‘yan shekarun nan, bisa manyan tsare-tsare tun bayan rikicin Ukraine.

A wata tattaunawa da shugaba Putin, Xi Jinping ya bayyana matsayin da kullum kasarsa ke tsayawa a kai da ma kokarin da take yi wajen ganin an warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. A cewarsa, muhimmiyar mafita ga rikicin Ukraine shi ne inganta gina wani sabon tsarin tsaro mai daidaito, inganci, da dorewa. Kasar Sin tana goyon bayan gudanar da taron zaman lafiya na kasa da kasa a kan lokaci, wanda kasashen Rasha da Ukraine suka amince da shi, tare da halartar dukkanin bangarori da dama, tare da yin tattaunawa cikin adalci kan dukkan shirye-shiryen da aka gabatar, kuma kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa kan warware matsalar Ukraine ta hanyar siyasa da wuri.

A nasa bangaren, Putin ya gabatar da matsayar Rasha kan wannan batu, yana mai cewa, kasarsa ta yaba da matsayin kasar Sin mai adalci da daidaito kan batun Ukraine. Ya kara da cewa, Rasha na kokarin warware matsalar din ta Ukraine ta hanyar siyasa, kuma tana son nuna sahihanci tare da ci gaba da yin mu’ammala da kasar ta Sin kan wannan batun. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments