Rasa tasiri a kasashen Afirka dake faransanci, ya sa Faransa karfafa alakarta da masu Ingilishi   

Wani bayyani da aka fitar ya nuna cewa kasar Faransa na karfafa alakarta da kasashen Afrika dake amfani da harshen Ingilishi saboda rasa tasirinta a

Wani bayyani da aka fitar ya nuna cewa kasar Faransa na karfafa alakarta da kasashen Afrika dake amfani da harshen Ingilishi saboda rasa tasirinta a kasashen dake magana da harshen faransanci.

Yanzu Emmanuel Macron yana mayar da dabarunsa zuwa ga kasashen da ke amfani da Ingilishi, yana fatan dawo da tasirin kasar da ya raunana a can baya a daidai lokacin da kyammar kasashen Yamma ke dada wanzuwa.

Bayan an kore ta a manyan biranen Afrika da dama, Paris yanzu tana komawa ga abokan huldarda masu amfani da harshen Ingilishi kamar kenya da Najeriya, kuma yarjejeniyar soja da ake shiryawa tsakanin Paris da Nairobi alama ce ta wannan.

An sanya hannu a kan yarjejeniyar a watan Oktoban 2025 tsakanin Kenya da Faransa, saidai dole ne Majalisar Dokokin Kenya ta amince da ita a watan Fabrairu.

A cewar shaffin Africa Intelligence, yarjejeniyar ta tanadi hulda ta soji, musayar bayanan sirri, hadin gwiwa, da tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Wannan ya zo ne yayin da aka tilasta wa Faransa ficewa daga kasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar wadanda ta yi wa mulkin mallaka.

Ana dai zargin hukumomin leken asiri na Faransa a ayyukan da ke kawo cikas ga tsaro a Afirka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments