Ramaphosa Ya Yi Tir Da Halin Yan Mulkin Mallaka Na Amurka, Ya Bukaci A Saki Madoro

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa yayi tir da gwamnatin kasar Amurka saboda halin mulkin mallaka da ta nuna a mamayar kasar Venezuela da

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa yayi tir da gwamnatin kasar Amurka saboda halin mulkin mallaka da ta nuna a mamayar kasar Venezuela da kuma satar shugaban kasar Nicolas Madoro da matarsa a ranar Asabar da ta gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaba Ramaphosa yana fadar haka a wani taron tunawa da wani dan gwagwarmaya na Jam’iyyar ANC a Jorhannersburg. Ya kuma yi kira ga kwamitin tsaro na MDD ta dauki matakai masu tsauri kan Amurka saboda abinda ta aikata. Ta kuma matakan da suka dace kan Amurka dangane shiga wata kasa mai cikekken yenci da kuma kujerar a majalisar.

Daga karshen shugaban ya bukaci kasashen duniya su hada kai don fuskantar Amurka a irin  halayen da ta bayyana a shugaban shugaba Donal Trump.

A ranar Asabar da ta gabata ce, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurni ga sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Venezuela daga cikin har da birnin Caracas babban birnin kasar inda suka kutsa da karfi cikin fadar shugaban kasa Nicolas Madoro suka kuma sace shi da kuma matarsa zuwa kasar Amurka, inda a halin yanzu suke fuskantar sharia kan wasu zarge-zargen karya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted