Rahoton INSS: Isra’ila’ za ta fuskanci barna mafi muni idan ta shiga yaki da Hizbullah

Cibiyar Nazarin Tsaro ta Isra’ila (INSS) ta gano cewa, idan Isra’ila ta shiga da Hizbullah gadan-gadan, to kuwa makaman Hizbullah zai yi babban lahali ga

Cibiyar Nazarin Tsaro ta Isra’ila (INSS) ta gano cewa, idan Isra’ila ta shiga da Hizbullah gadan-gadan, to kuwa makaman Hizbullah zai yi babban lahali ga Isra’ila

Cibiyar da ta fi mayar da hankali kan tsaro a Haramtacciyar Kasar Isra’ila, inda a wanann karon ta yi nazari kan illolin da fadace-fadacen da ake yi ci gaba da yi ke ahifarwa yahudawa mazauna yankin arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye.

A halin yanzu wannan batu yana da matukar muhimmanci a cewar cibiyar, yayin da jami’an Isra’ila ke barazanar shiga yaki da kasar Labanon, wanda kai iya haifar da mummunan sakamako ga yahudawa ‘yan share wuri zauna.

INSS ta bayar da rahoton cewa, Hizbullah ta harba sama da makamai 5,000 zuwa Isra’ila tun 8 ga Oktoba, 2023. Wannan ya hada da manyan makamai kamar roka artillery da sauransu, da kuma makamai masu linzami samfurin ATGM.

Wadannan hare-haren sun haddasa barna mai yawa ga yahudawa da ta hada da hasarar rayuka da jikkata da kuma asarar dukiyoyi masu a cewar rahoton wannan cibiya.

Duk da haka, INSS ta mayar da hankali kan illolin da hare-haren suka haifar a matsugunai da kuma babban birnin yankin Kiryat Shmona.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments