Kafofin yada labarai daga Isra’ila na tabbatar da kutsen da akayi wa kasar akan wasu takardun bayyanan sirrin shirinta na nukiliya.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Iran ta ce ta samu tarin takardun sirri da suka shafi ayyukan nukiliyar Isra’ila.
Ministan leken asirin kasar Iran Esmail Khatib ya ce tarin takardun sirri na Isra’ila da kasar ta samu na da alaka da makaman nukiliyar gwamnatin kuma za su kara karfi ga tsarin garkuwa daga hare-haren sama na Iran.
“Takardun da muka samu na da alaka da bayanai game da cibiyoyin nukiliyar su,” kamar yadda Khatib ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na IRIB.
Kafafen yada labaran Isra’ila sun tabbatar da hakan, tare da bayyana shi a matsayin “babban kutse.”
Ba tare da bayar da karin bayani ba, wadannan majiyoyin sun bayyana cewa “dubban takardu ne da suka shafi tsare-tsare da na’urorin nukiliya na gwamnatin Sahayoniya.”
Saidai ma’aikatar harkokin soji ta Isra’ila ba ta ce uffan ba kan lamarin.
Tashar talabijin ta 12 ta Isra’ila ta tabbatar da cewa Tehran ta yi nasarar samun wasu muhimman bayanai da ke da alaka da shirin nukiliyar Isra’ila,