Ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta sanar da cewa, yarjejeniyar tsagaita wutar ta Gaza za ta fara aiki ne a yau Lahadi da karfe 8:30 na safe agogon Gaza, 6:30 agogon GMT.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari ne ya sanar da hakan a dandalin sada zumunta na X, inda ya ce: “Bayan daidaitawa tsakanin bangarorin da ke cikin yarjejeniyar da masu shiga tsakani, za a fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, a zirin Gaza ne daga karfe 8:30 na safiyar yau Lahadi 19 ga watan Janairu. “
Ya kuma bukaci mazauna yankin da su “yi taka tsantsan, sannan su jira umarni daga majiyoyin hukumomi na yankin.
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar dakatar da bude wuta ne, a hukumance tare da bangaren kungiyar Hamas, bayan amincewar karamar majalisar ministocin tsaro ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila da yarjeniyar.
A fadin shafin labarai na Axios, ministocin Isra’ila 24 ne suka kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar, a yayinda wasu 8 suka nuna adawa da hakan.