Qalibaf: Jinin Shahid  Kassim sulaimani Ya  Karfafa Gwgawarmaya A Duniya

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya fadi cewa, Shahid Kassim Sulaimani ya kasance mutumin da yake  daukar damammaki a cikin yanayi

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya fadi cewa, Shahid Kassim Sulaimani ya kasance mutumin da yake  daukar damammaki a cikin yanayi mafi tsanani na kalubale da barazana, a lokacin da sauran mutane suke zama ‘yan kallo.

A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Laraba ya ce; A yau muna juyayin tunawa da shahadar gwarzon fada da ta’addanci, wanda miliyoyin mutanen duniya masu son adalci a duniya suke kauna, Shahid Kassim Sulaimani, tare da abokin gwgawarmayarsa Injiniya Abu Mahdi.”

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce, Shahadar tana nufin ci gaba da fadadar gwagwarmaya a duniya ba kawo karshenta ba.

Muhammad Bakir Qalibaf ya kuma ce; Shahadar da Kassim Sulaimani ya yi a hannun Amurkawa masu laifi, ya tabbatar da cewa jinin shahidin tamkar shuka ce  ta gwagwarmaya wacce ta tsiro ta girma.

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran  ya kuma ce; Matukar tunanin yin gwgawarmaya yana nan a duniya, kuma matukar ana ci gaba da yin gangami a duniya domin yin kira da a ‘yanto da Falasdinu, to koyarwar shahid Haj Qassim tana nan a raye.”

A ranar  3 janairu na 2020 ne dai Janar Kassim Sulaimani da Shahid Injiniya Abu Mahadi na Iraqi su ka yi shahada sanadiyyar harin da Amurka ta kai musu a kusa da filin saukar jiragen sama na birnin Bagadaza a kasar Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted