Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran bata adawa da hanyar diblomasiyya, amma dole ne ta kasance ta bangarori biyu masu yenci, da kuma mutunta juna.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a hirar da ta hada shi da tashar talabijan ta CNN wanda aka watsa a yau Alhamis. Ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tabbatar da cewa shi yana son ya fada kuma a bi kawai, idan ba haka ba zai yi amfani da karfi don cimma manufofinsa a kan kasar Iran.
Qalibaf ya ce a cikin watan yunin shekarar da ta gabata, kasashen biyu suna cikin tattaunawa Amurka da HKI suka kaiwa kasar hare-hare, wanda ya nuna yaudara da kha’inci a fili. Babban jami’in siyasa na kasar ta Iran ya kammala da cewa, Iran ba zata amince da karban umurni daga kasar Amurka ba zata amince da kama karya ba. Saboda an kafa kasar saboda rashin amincewa da hakan.
Yace idan Trump yana neman zaman lafiya to kuwa ya san hanyar, idan kuma ba haka ba, to kuwa Iran ba zata jada baya a matsayinta na kasa mai cikekken yenci ba.