Pezeshkiyan: Mun Je Taron MDD Ne Domin Tattaunawa Da Kare Hakkokin Al’ummar Iran

Shugaban kasar Iran Dr. Mas'us Pezeshkiyan ya bayyana cewa; Mun je taron MDD ne domin tattaunawa da kuma kare hakkokin al'ummar Iran da kuma bayyana
shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Iran Dr. Mas’us Pezeshkiyan ya bayyana cewa; Mun je taron MDD ne domin tattaunawa da kuma kare hakkokin al’ummar Iran da kuma bayyana mahangar kasarsu akan abububuwan da suke faruwa a duniya da kuma yankinmu.”

Shugaban na kasar Iran ya fada a jiya Laraba cewa; A cikin jawabin mun yi kokarin bayyana yadda al’amurra suke bisa la’akari da maganganun da su ka fito daga bakin shugaban kasar Amurka na kiyayya ga al’ummar Iran,domin sanar da duniya gaskiyar da take a kasa.

Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; Halayyar da Amurkan ta nuna ba ta dace ba da dokokin kasa da kasa ko kuma ‘yan’adamtaka,saboda yadda ta mayar da karfi shi ne hanyar mu’amalarta da duniya a cikin shekarun bayan nan, mun kuwa ga misalan haka a kasashen Venezuela, Cuba da kuma Greenland.

Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce; Amfani da karfi wata hanya ce da tarihin Amurka ya ginu akanta, to amma a bayan nan ya fi fitowa fili ta yadda ake Magana akan rusa da shafe wata Daula.”

Bugu da kari shugaba Pezeshkiyan ya ce; Iran kasa ce mai dogon tarihi da ci gaba mai zurfi, babu yadda za a iya rusa ta.kuma duk da matsin lamba mai tsanani da al’ummar Iran suke fuskanta, suna ci gaba da yin tsayin daka wanda ya cancanci yabo.

Shugaban na kasar Iran ya kuma yi Magana akan kisan gilla wanda Isra’ila ta yi a Iran da ya shafi masana da jami’an gwamnati wanda aiki ne na ta’addanci. Kamar kuma yadda ya yi Ishara da irin wadannan kashe-kashen na Isra’ila a cikin Lebanon da Gaza dake cin karo da dokokin kasa da kasa. Haka nan kuma kashe fararen hula wanda an fitar da rahotanni akansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted