Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Taron koli na Shanghai wata muhimmiyar dama ce ta bunkasa huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi la’akari da karfafa dangantaka da kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) daya daga cikin manufofin ziyararsa a kasar China da halartar wannan taro. Ya ce, taron kolin na Shanghai wata dama ce mai matukar muhimmanci da kuma dacewa don inganta huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya da sauran kasashe.
Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya bayar da safiyar Lahadi a filin jirgin sama na Mehrabad na Tehran kafin ya tashi zuwa kasar China don halartar taron kolin Shanghai: Kasashe mambobin kungiyar Shanghai sun kai kimanin mutane biliyan 2.5 a duk fadin duniya, kuma fiye da kashi 40% na tattalin arzikin duniya ya fada cikin tsarin wannan kungiya.
Ya kuma jaddada cewa; Wannan taron kolin wani kokari ne na karfafa hadin gwiwa wajen gudanar taimakekkeniya tsakanin bangarori daban-daban da kuma tunkarar tsarin bai daya ga mulkin kama-karya da Amurka da wasu kasashen Turai ke yi a duniya. Ya kara da cewa, “A irin wannan taron, ana iya inganta dangantakar da ke tsakanin kasashe mambobin kungiyar da sauran kasashe.