Petro: Man fetur shine burin Amurka a Venezuela ba yaki da fataucin kwayoyi ba

Yayin da ayyukan sojin Amurka ke karuwa a yankin Caribbean da Pasifik, shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya zargi gwamnatin Trump da yin amfani da

Yayin da ayyukan sojin Amurka ke karuwa a yankin Caribbean da Pasifik, shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya zargi gwamnatin Trump da yin amfani da matsin lamba kan kasar Venezuela da sunan yaki da fataucin muggan kwayoyi a matsayin hujjar samun damar shiga kasar don mamaye  albarkatun man fetur da Allah ya huwace wa kasar.

Man fetur shine tushen al’amarin, Petro ya fadawa CNN a cikin wata hira ta musamman, yana mai cewa Venezuela ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan danyen ma a duniya.

“Saboda haka, wannan batun baki dayansa a kan man fetur ne. Na yi imani cewa (Shugaban Amurka Donald Trump) na tunanin yadda zai samu mai a kasar Venezuela ne ba batun dimokiradiyya ko yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi ba ne, “in ji shi.

Petro ya bayar da hujjar cewa man fetur na Venezuela ya kasance a sahun gaba game da manufofin Amurka. Ya bayyana cewa kadan ne kawai na cinikin magunguna a duniya ke bi ta kasar Venezuela kuma ba a daukar kasar a matsayin babbar mai samar da su.

A ranar Talata, Petro ya zargi Amurka da yunkurin dawo da wani sabon mulkin mallaka a kan kasashen latin.

Da yake mayar da martani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya ce gwamnatin Trump za ta ci gaba da ayyukanta na yaki da muggan kwayoyi a yankin Caribbean da kuma jajircewarta na kare Amurkawa daga abin da ya kira mummunar gubar gwamnatin Maduro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments