Paparoma Leo 14, Da Firay Ministan Espania Sun Yi Tir Da Yaki Kan Iran Sunce Baya Bisa Doka

Paparoma Leo 14, ya bayyana a jiya Asabar kan cewa, yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a karshen watan Fabrayrun da ya

Ofishin Jakadancin Iran A Ghana Ya Mayar Da Martani Kan Cin Zarafin Trump Ga Paparoma

Paparoma Leo 14, ya bayyana a jiya Asabar kan cewa, yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a karshen watan Fabrayrun da ya gabata baya daga cikin yake-yaken da suka hallata.

Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran da nakalto paparoman yana fadar haka a tattaunawar da yayi da yan jarida a cikin jirginsa a kasar Espaniya a jiya Asabar.

Paparoman ya bayyana haka ne a lokacinda wani dan jarida ya tambayeshi dangane da halaccin yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran.

Jaridar Politico ta nakalto paparoman yana cewa yakin baya daga cikin halattancen yaki kuma baya bisa doka.

Jawabin paparoman dai yana maida martani ga maganar mataimakin shugaban kasar Amurka J.D. Vance wanda yake magana kan cewa yakinsu kan JMI ya halatta.

A ganawarsa da firai ministan kasar Espania Lio 14 da Firay ministan duk sun tabbatar da cewa yakin Amurka da HKI kan Iran baya bisa ka’ida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted