Nuri Al-Maliki Ya Jajurce Kan Matsayinsa Na Tsayawa Takarar Fira Ministan Kasar Iraki

Al-Maliki ya tabbatar da jajircewarsa na tsayawa takarar fira ministan ƙasar Iraqi kuma ya ƙi amincewa da batun janyewa Nouri al-Maliki, shugaban tawagar ƙungiyar Daulatul-Qanun

Al-Maliki ya tabbatar da jajircewarsa na tsayawa takarar fira ministan ƙasar Iraqi kuma ya ƙi amincewa da batun janyewa

Nouri al-Maliki, shugaban tawagar ƙungiyar Daulatul-Qanun ta Ƙasa a Iraki, ya sake nanata aniyarsa ta tsayawa takarar fira ministan kasar, yana mai ƙin amincewa da duk wani batun janyewa daga kan matsayinsa saboda matsin lamba daga waje. Ya jaddada cewa: Dangantakar Iraki da Iran ta dogara ne akan muradu da masalahar da suka yi tarayya a kai.

A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran AFP, Maliki ya ce, “Ba shi da niyyar janyewa kwata-kwata daga kan aniyarsa,” yana mai tabbatar da cewa tawagarsu ta amince da naɗinsa kuma yana ci gaba da jajircewa a kanta har zuwa ƙarshe. Ya kuma yi watsi da duk wani tsangwama daga wajen kasar da tantance wanda za a zaɓa a Iraki.

Dangane da dangantakar ƙasashen waje, Maliki ya nuna cewa: Dangantakar Iraki da Iran ta dogara ne akan muradu da masalahar da ta hada su, yayin da ya jaddada muhimmancin dangantakar da ke tsakanin Iraki da Amurka a fagen ci gaban ƙasar, tare da alƙawarin da Iraki ta yi na kare dukkan ofisoshin diflomasiyya da ofisoshin jakadancin kasashen waje a kasarta, tare da hana duk wani keta musu haddi daga kowace ɓangare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted