Mazauna babban birnin jamhuriyar Nijar, Yamai sun bayyana yadda su ka ji karar harbe-harben bindigogi na tsawon sa’o’i a cikin dare.
Wani shaidai ganin ido ya fada wa manema labaru cewa an ji karar fashewar abubuwa masu karfi a tsakar daren Alhamis a kusa da filin saukar jiragen saman a Diori Hamani, kafin daga baya karar da rika raguwa sannu a hankali.
Wani matashi mai suna Ibrahim Bubakar wanda yake rayuwa a kusa da filin saukar jiragen saman ya fadi cewa;
” Kowa ya fada cikin rudani. Da fari mun zaci ko matsalar wutar lantarki ce, ko kuma wasan wuta ake yi. To amma daga baya mun yi mamakin yadda lamari ya ci gaba mun gane cewa wani abu ne na daban, ‘yan ta’adda ne su ka kawo hari.”
Wani matashin kuwa ya ce; “Mun tsorata. Kuma da yara a kusa da ni, duk muna rike da carbi muna ta rokon Allah ya kare mu, muna kuma rokon dukkanin ‘yan kasa akan su yi ta yi wa kasarmu Nijar addu’a.”
Sai dai a wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa; Maharan ‘yan ta’adda ne, kuma an kashe 20 daga cikinsu, yayin da su kuma su ka kashe sojojin kasar biyu. Bugu da kari, jami’an tsaron na Nijar sun yi nasarar kama wasu ‘yan ta’addar su 11.
Kungiyoyin da suke ikirarin jihadi a yankin Sahel, sun addabin kasar ta Nijar da sauran kasashen da suke makwambata da ita. Kungiyoyin kan yi amfani da girman yankunan dake kan iyakokin, Nijar, Mali da Burkina Faso, wajen kai da komowa.