Shugaban kasar ta Nigeria, Bola Ahmad Tinubu ne tabbatar da cewasSabuwar dokar za ta fara aiki daga farkon wannan watan na Janairun duk da sukar da a ka yi wa dokar.
Bayan cire kudin tallafi na man fetur da kuma raguwar kimar kudin kasar Naira a shekarar farko da ya zama shugaban kasa, Bola Tinbu ya fito da sauye-sauye a cikin tsarin haraji a karkashin shirinsa na sabunta tattalin arziki.
Wasu ‘yan majalisar kasar suna zargin cewa an shigar da wasu sabbin tsare-tsare a cikin Shirin na haraji, bayan da majalisar ta amince da shi, tare da bayyana hakan a matsayin yiyuwar keta doka.
Sauye-sauyen da aka shigar daga baya sun hada da bai wa mahukunta karfin ikon kwace kaddarorin mutane ba tare da umarnin kotu ba, da kuma biyan diyya ta tilas,kamar yadda ‘yan majalisar su ka yi zargi.
Sai dai shugaban kasar ya yi watsi da wannan zargin yana mai kara da cewa, babu wani dalili da zai sa a jinkirta fara aiki da dokar. Haka nan kuma ya yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran ‘yan kasa da su bayar da goyon baya ga aiki da Shirin.
Shugaban kasar ya kuma yi alkawalin yin aiki da bin ka’idojin aiki domin warware damuwar da ‘yan majalisar suke da ita.
Shugaban Kwamitin Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce mutane za su bayyana kudin shigarsu da kansu sannan su biya haraji a inda ya dace. Ya bayyana cewa tsarin yana da sauki, bayyananne, kuma ba zai wahalar da talakawa ba.