Nigeria: Harin Bokoharam Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Da Dama A Arewacin Nigeria

Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar sun ambaci cewa; Kungiyar ta bokoharam ta kai hari a garin “Bogabu’ da

Rahotanni da suke fitowa daga Jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar sun ambaci cewa; Kungiyar ta bokoharam ta kai hari a garin “Bogabu’ da kuma Mayo-Ladde.”

Maharan dai sun yi amfani da babura ne wajen kai hari, bayan da su ka ci karfin masu aikin bayar da tsaro a yankin.

A garin Bugaro an kashe mutane 11, sai kuma wasu 9 a garin Mayo Ladde.

Bugu da kari, ‘yan kungiyar ta bokoharam sun yi wawason kayan abinci tare da kunna wuta a cikin gidaje da shaguna.

 Kungiyoyin Bokoharam da Da’ish, ( ISIS) sun addabi yankin arewa maso gabashin kasar Nigeria, yayin da ‘yan barayin daji dake neman kudin fansa su ka addabi arewa maso yammacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted