Nazari Ya Bayyana Cewa; Adadin Falasdinawa Da Aka kashe A Gaza ya shige Wanda Ake Watsawa

Nazarin likitanci ya bayyana cewa: Yawan Falasdinawan da suka yi shahada a Gaza ya haura kashi 40 cikin dari da alkaluman ma’aikatar lafiyar Falasdinu ke

Nazarin likitanci ya bayyana cewa: Yawan Falasdinawan da suka yi shahada a Gaza ya haura kashi 40 cikin dari da alkaluman ma’aikatar lafiyar Falasdinu ke watsawa

Wani bincike da mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ta buga a yau Juma’a ya watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza a cikin watanni 9 na farkon yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Gaza, ya zarce kashi 40 cikin dari idan aka kwatanta da adadin da ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinu ta sanar.

Har zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar da ta gabata, ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta watsa rahoton cewa: adadin wadanda suka yi shahada a yakin ya kai 37,877.

Sai dai sabon binciken wanda ya samo asali daga bayanan ma’aikatar, wani bincike na yanar gizo da kuma bayanan da suka shafi kafofin sada zumunta, ya kiyasta cewa adadin wadanda suka yi shahadan sakamakon samun raunukan yaki a Gaza ya kai tsakanin shahidai 55,298 da 78,525 a cikin wannan lokacin.

Mafi kyawun ƙiyasin adadin waɗanda suka yi shahadan a cikin binciken shi ne 64,260, wanda ya yi daidai da sama da kashi 41cikin dari da alkalumman da ma’aikatar lafiya ta buga na wancan lokacin.

Bisa kididdigar da kungiyar masu bincike da kasar Birtaniya ta jagoranta ta tabbatar da cewa: Kashi 59 cikin dari na wadanda suka yi shahadan mata ne da yara da kuma tsofaffi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments