Natanyahu Ya Ce Makamai Masu Linzami Masu Keta Nahiyoyi Na Iran Barazana Ce Ga Amurka

Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana gargadin Amurka kan abinda ya kira, makamai masu linzami masu keta

Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana gargadin Amurka kan abinda ya kira, makamai masu linzami masu keta nahiyoyi wadanda JMI take ginawa barazana ce ga Amurka. Ya ce makaman suna iya isa biranen Amurka daga cikin har gidan Trump da ke ‘Mar-a-Lago’, a bakin ruwa na Palm Beach a jihar Florida.

Daily mail ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a hirar da ta hada shi da wani dan jirada mai suna Ben Shapiro. Ba tare da bada wata hujja ko dalili ba, Natanyahu ya ci gaba da cewa, makaman wadanda suke iya zuwa wurare masu nisan kilomita 800 zasu kai biranen washington da kuma NewYork har da kuma gidan shugaba Trump dake Palm Beach.

Labarin ya kara da cewa JMI tana da makamai masu linzami wadanda suke iya kai wa tazarar kilomita 2000, kuma ta yi amfani da wasu daga cikinsu a yakin kwanaki 12 da HKI a cikin watan Yuni na wannan shekarar. kuma masana sun tabbatar da cewa makamanta masu linzamin zasu iya kaiwa kan dukka kasashen Turai.

Iran ce a kadai a yankin gabas ta tsakiya ta mallaki iran wadannan makamai masu cin dogon zango.

Gwamnatin JMI dai ta sha nanata cewa makamanta ba abin tattaunawa bane da kowa a duniya, saboda makamanta tsaron kasarta ne.

Amma kasashen Turai na E3 sun sake dorawa JMI takunkuman MDD kafin yarjeniyar JCPOA ta shekara ta 2015, tare da bukatar ta rage nisan makamanta masu linzami zuwa tazarar kilomita 500 kacal.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments