Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa shirin garkuwan makamai na HKI ya rushe bayan hare haren maida martani wadanda JMI ta kai kan haramtacciyar kasar a ranar 14 ga watan Afrilin da ya gabata.
Sayyid Nasarallah ya bayyana haka ne a wani jawabin da ya gabatar a jiya litinin, a ranar tunawa da shahid Sayyed Mustafa Badreddine daya daga cikin kwamandojin mayakan hizbullah, wanda yayi shahada shekaru 8 da suka gabata.
Ya kuma kara da cewa hare haren maida martanin da JMI ta kai kan HKI ya raba kan kwamadojin sojojin HKI, don idan sun tsada yaki an sami nasara a kansu, sannan idan sun ci gaba da yakin zasu kai kansu ga halaka ne.
Sayyid Nasarallah ya kara da cewa yakin Tufanul Aksa ya sauya duniya ya kuma sanyata gaba dayanta tana tunanin al-ummar Falasdinu kuma saboda wannan yakin a halin yanzu matsalar al-ummar Falasdinu it ace babbar matsala abin tattaunawa a duk duniya. Banda haka wannan yakin ya sanya kasashe 140 a duniya suna goyon bayan samuwar kasar Falasdinu mai cikekken yenci.
Daga karshe ya bayyana cewa juriyar da Mata da yara suka yi kuma suke yi a yakin gaza ya sa a dole duniya ta maida hankali kan al-amarin Falasdinu da falasdinawa.