Yansanda a jihar Kaduna na tarayyar Najeriya sun kama mutane 523 a jihar, wadanda ake tuhuma da ayyukan sace mutane da kuma garkuwa da su don karban kudaden fansa.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa, mutane 26 daga cikinsu yan fashi da makami ne, wadanda suke satar mutane su yi garkuwa da su don neman kudaden fansa.
12 daga cikinsu masu satar shanu, sannan 97 daga cikinsu masu satar wayoyi.
17 kuma masu satar motoci, sannan 10 kuma masu pyade da sauransu.
Kwamishinan yansanda na jihar Kaduna CP Ibrahim Abdullahi ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da yan jaridu a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa an kama mutane 350 daga cikin wadannan masu aikata laifuka ne a hare haren da yansanda suka kai masu a mabuyansu a cikin jihar.