Kamfanin NNPCL mai kula da al-amuran makamashi a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa mai yuwa farashin man fetur a gidajen manta a duk fadin kasar su wuce naira 1000 kan ko wace lita.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa a cikin rahoton da kamfanin ya bayar yace a halin yanzu ya fara sayan tataccen man fetur daga matatan man Dangote, kuma kamfanin zai biyu kamfanin dangote ne da dalar Amurka na man da ta saya a cikin watan satumban da muke ciki sannan sai ranar 1 ga watan Octoba ne za’a fara sayan man da naira.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu wannan shi ne farashin lita guda na man fetur a gidajen man kamfanin a duk fadin kasar.
Lagos, N950 kan ko wace lita, Sokoto, N992 kan ko wace lita; Oyo, N960 kan ko wace lita; Kano, N999; Kaduna, N999; Abuja, N992; Rivers, N980; da kuma Borno, N1019.
Daga karshe kamfanin ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin tarayyar bata da hannun wajen sasantawa kan farashin makamashi a kasar. Yan kasuwa ne suke sasantawa a tsakaninsu da kamfanonin masu tatan man fetur a ciki ko wajen kasar.