Najeriya: Majalisar Wakilai Ba Ta Yanke Hukunci Kan Kudirin Harajin Tinubu Ba

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta samar da matsaya kan sabon ƙudirin harajin da Tinubu ya aike musu. Sai

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta samar da matsaya kan sabon ƙudirin harajin da Tinubu ya aike musu.

Sai dai, ya ce majalisar za ta yi aiki da kundin tsarin mulki don tantance duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara, a inda ya zama tilas.

Majalisar ta bayyana muhimmancin sauya fasalin tsarin haraji a Najeriya domin samar da tattalin arziki mai ɗorewa da rage dogaro da rancen kuɗi.

A gefe guda, majalisar ta jaddada cewa, Najeriya na da karancin haraji idan aka kwatanta da tattalin arzikinta, inda yawan harajin ya tsaya a kashi 6, yayin da matsakaici haraji a duniya yake a kashi 15.

A cewar majalisar akwai buƙatar a magance hakan domin samar da kudaden  gudanar da ayyuka kamar ilimi, lafiya, da gine-gine.

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Kudi da Sauya Fasalin Haraji, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa, a 2020, kashi 97 na kudaden  shiga na Najeriya ya tafi ne wajen biyan bashi, yayin da hauhawar farashi ya kai kashi 33.

A watan da ya gabata ne fadar shugaban kasa, ta aike wa majalisun dokoki kudurorin, amma kuma majalisar zartarwa ta bayar da shawarar kin amincewa da kudurorin saboda wasu sarƙaƙiya da ke tattare da su. Duk da haka, Tinubu ya ki amincewa ya janye kudirin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments