Najeriya: Majalisa Ta Sa A Kamo Shugaban Kamfanin Julius Berger Kan Zargin Almundahanar N141bn

Majalisar Dattawa ta sa a kamo Manajan Daraktan Kamfanin Gine-gine na Julius Berger kan badaƙalar aringizon Naira biliyan 141 a aikin gyaran titi Shugaban Majalisar,

Majalisar Dattawa ta sa a kamo Manajan Daraktan Kamfanin Gine-gine na Julius Berger kan badaƙalar aringizon Naira biliyan 141 a aikin gyaran titi

Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce ’yan majalisar sun ba da umarnin ne saboda sau uku Shugaban Kamfanin na kin amsa gayyatar majalisar.

Majalisar ta gayyaci shugaban kamfanin ne kan zargin ƙara Naira biliyan 141 a kuɗin aikin babban titin Itukpani zuwa Itu da ke jIhar Enugu, tare da yin watsi da aikin.

Da yake gabatar da ƙudurin, Mai Tsawatarwan Majalisa, Sanata Osita Ngwu, ya zargi kamfanin da ƙara kuɗin aikin daga Naira biliyan 54 zuwa biliyan 195.

Dan majalisar ta bayyana cewa daga bisani kamfanin ya kwashe kayansa daga wurin da ake aikin.

A kan haka ne sau uku majalisar taba gayyatar shugaban kamfanin na Julius Berger ya zo ya yi bayani, amma ya yi watsi da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments